Overview of IDEAS Program in Hausa
Shirin IDEAS shiri ne na Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Jamiar Baze da Kamfanin Domenium wanda aka tsara Shirin don horas da matasa akan wasu bangarori na Fasahar Sadarwa ta Zamani (ICT). An tsara Shirin yadda za’a horas da mahalarta Shirin a matakin Difilomar Kwarewa (Professional Diploma) a bangarorin Cybersecurity, Blockchain Technology, Data Analysis, Artificial Intelligence, Business Inteligence and Dashboard Creation da kuma Software Engineering.
Jihar Jigawa a karkashin Hukumar Samar da Ayyukan yi da Dogaro da Kai ta rungumi Shirin inda da samo damammakin da za’a horas da matasa guda dubu daya a bangarorin fasahar da suke da sha’awa a fadin Jihar Jigawa. Horon zai kasance tsawon wata shida ana koyon aiki da kuma wata shida na gabatar da abinda aka koya a wajen aiki wato Internship.
Za’a gabatar da horon a Cibiyoyin Fasahar Sadarwa guda 15 wanda Hukumar NITDA ta gina a fadin Jihar Jigawa.
PROFESSIONAL DIPLOMA IN SOFTWARE ENGINEERING
Mahalarta wannan tsarin zasu koyi yadda ake tsara bayanan da ake sarrafa computer da su wato programming, zasu koyi amfani da mahajoji irinsu Webstorm, Visual Studio, Visual Studio Code da sauransu. Bayan haka mahalartan za su koyi yaren da ake rubuta bayanan sarrafa computer irinsu C#, Java, Python da sauransu.
A karshen horarwas mahalartan za su samu damar zama kwararrun Software engineers masu rubuta programs wanda manyan kamfanoni da ma’aikatu zasu iya daukarsu aiki na dindindin ko na wicingadi. Matsakaicin albashin Software Engineer a yanzu shine N250,000 a wata.
PROFESSIONAL DIPLOMA IN CYBERSECURITY
Mahalarta wannan tsarin zasu koyi yadda ake bada kariya ga Computer Network daga yan dandatsa wato hackers, zasu fahimci yadda ake kawowa Computer networks hari da kuma yadda ake tsare harin. A karshen horon mahalartan zasu kasance masu gadin internet da duk wani abu da ya shafi bada tsaro ga computer network. Mahalartan zasu koyi abubuwan da suka shafi encryption protocols, cryptography techniques, system authentication protocols, system auditing da kuma penetration testing.
Akwai damammamkin samun aiki masu yawa ga Cybersecurity Experts kuma matsaikaicin albashin wanda yak ware a bangaren Cybersecurity shi ne N300,000 a wata.
PROFESSIONAL DIPLOMA IN DATA ANALYTICS
Wadanda suka shiga wannan tsarin za’a horar da su a kan yadda ake tattara kananan bayanai (data) don a samar da bayanai masu ma’ana kuma masu amfani. Mahalartan zasu koyi amfani da manhajar Tableau wajen bayyanar da kananan bayanai (Data Visualization). Bayan haka mahalartan zasu koyi abinda ake kira da Big Data ta hanyar amfani da manhajoji irinsu Hadoop, Hive, Spark da IBM Watson, sannan kuma zasu koyi sarrafa bayanai da kayan aiki irinsu Python, SQL, R da Microsoft Excel. Akwai damammakin ayyuka masu yawa wadanda wanda suka samu horo suka zama Data Analyst zasu iya samu kuma mafi karancin matakin albashin Data Analyst ya fara daga N250,000 a wata.
PROFESSIONAL DIPLOMA IN BUSINESS INTELLIGENCE AND DASHBOARD CREATION
Wadanda suka shiga wannan tsarin za’a horar da su akan tsara bayanan kasuwanci da kuma fitar da allon bayanai (business intelligence and dashboard). Mahalartan zasu koyi amfani da manhajojin Tableau da PowerBI sannan kuma zasu samu horon wajen iya gabatar da bayanai (presentation skills) don amfani da bayanai wajen cigaban kasuwanci. Bayan haka zasu koyi koyi sarrafa bayanai da kayan aiki irinsu Python, SQL, R da Microsoft Excel. Akwai damammakin ayyuka masu yawa wadanda wanda suka samu horo suka zama Business Intelligence and Dashboard Creation Professionals zasu iya samu kuma mafi karancin matakin albashin Business Intelligence and Dashboard Creation Professionals ya fara daga N350,000 a wata.
PROFESSIONAL DIPLOMA IN APPLIED ARTIFICIAL INTELLIGENCE
Mahalarta wannan tsarin zasu samu horon a bangaren abinda ya shafi sabuwar fasahar da take Shirin canja duniyar Fasaha. Artificial Intelligence shi ne samar da computer mai tunani kuma mai koyo kwatankwacin yadda dan-adam yake tunani da koyo. Wadanda za’a horar zasu samu kwarewa wajen samar da sababbin Artificial Intelligence a bangarorin Kiwon Lafiya, harkokin Kudi, Kere-kere da kasuwanci. Za’a horar dasu abubuwan da suka shafi machine learning algorithms, neural networks, natural language processing da kuma computer vision. Ana hasahen Fasahar AI zata samu mazauni a dukkan wasu bangarori na rayuwa kuma akwai damammakin ayuuka masu yawa a wannan bangaren. Wadanda suka samu horo kuma suka kware abangaren AI suna samun matakin albashi nafi karanci daga N400,000 zuwa sama.
PROFESSIONAL DIPLOMA IN BLOCKCHAIN TECHNOLOGY
Mahalarta wannan tsarin zasu samu horon a bangaren abinda ya shafi Blockchain Technology. Blockchain Technology shine sabuwar fasahar da ta shafi bangaren abinda ake kira cryptocurrency da sauran fasahohi da ake amfani da su wajen musayar bayanai a cikin sirri. Mahalarta wannan tsarin zasu samu kwarewa a wannan bangare kuma zasu koyi abubuwa da suke da alaka da decentralised finance (DeFi) da kuma gabatar da kasuwanci a karkashin tsarin Web 3.0, akwai dammamkin ayyuka masu yawa a karkashin Blockchain Technology.
Domin shiga tsarin danna wannan maballin
https://www.yeea.jg.gov.ng/programs/details/ict-program-cohort-2